Kungiyar EU ta cimma yarjejeniya akan daftarin kundin tsarin mulki | Siyasa | DW | 19.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kungiyar EU ta cimma yarjejeniya akan daftarin kundin tsarin mulki

Tarayyar turai ta kawo ƙarshen taƙaddama kan batun kundin tsarin mulkin ta bayan tsawon shekaru biyu suna jayayya

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Portugal Jose Socrates mai riƙe da shugabancin kungiyar EU

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Portugal Jose Socrates mai riƙe da shugabancin kungiyar EU

Tarayyar turai ta kawo ƙarshen taƙaddamar da ta hana ruwa gudu game da kundin tsarin mulkin ta. Waɗannan sune irin kalaman da suka fito daga Lisbon mai riƙe da shugabancin karɓa karɓa na ƙungiyar tarayyar turan, bayan da shugabanin ta suka cimma yarjejeniya ta yin kwaskwarima ga kundin tsarin ƙungiyar. P/M Portugal Jose Socrates mai riƙe da shugabancin ƙungiyar yace wannan nasara ta kawo ƙarshen dambarwar da dabaibaye ƙungiyar tun bayan da ƙasashen Faransa da Netherland suka yi watsi da daftarin kundin tsarin mulkin a ƙuriár raba gardama da jamaár su suka kaɗa a shekarar 2005.

Jose Socrates ya shaidawa yan jarida cewa wannan yarjejeniya a yanzu, ta ɗora tarayyar turan kan tafarkin cigaba. Yace shugabanin ƙasashe 27 na tarayyar turan za su hallara a Lisbon a ranar 13 ga watan Disamba domin rattaba hannu a kan yarjejeniyar a hukumance.

Shugabanin tarayyar turan sun dai cimma wannan yarjejeniyar ce bayan tataɓurza da ƙasashen Poland da Italiya waɗanda aka sami shawo kan su da gumin goshi. Poland ta sami sahalewa cewa ƙananan ƙasashe na iya hawa kujerar naƙi a mataki na wucin gadi domin jinkirta zartar da wasu hukunci da ƙungiyar tarayyar turan ka iya ɗauka. Yayin da shi kuma P/M Italiya Romano Prodi ya sami ƙarin kujera guda a majalisar dokokin tarayyar turai a matsayin masalaha inda ƙasar sa ke da ƙarancin wakilai a majalisar dokokin, idan aka kwatanta da manyan ƙasashe irin su Britaniya da Faransa.

A dangane da wannan nasara, Shugaban hukumar tarayyar turan Jose Manuel Barosso yayi bayani da cewa a wannan karon, babu wasu dalilai ko hujja ga shugabannin ƙasashen da gwamnatoci na ƙin amincewa da yarjejeniyar. yace Wannan babbar nasara ce. Ya kara da cewa da ƙwaƙwarar ƙudiri da manufa ta haɗin kan turai za su iya warware dukkan wasu matsalolin su

Daftarin yarjejeniyar dai na da nufin maida hankali da bada kulawa sosai ga matakan ƙololuwa na zartar da shawarwari da suka shafi tarayyar turai, a karon farko tun bayan da ƙungiyar ta karɓi sabbin ƙasashe goma a cikin ta, a shekarar 2004, kana a watan janairu na wannan shekarar kuma aka shigar da ƙasashen Bulgaria da Romania.

Ita ma da take tsokaci a yayin wani taron manema labarai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana cewa ta yi baá sami wani wanda ya baiyana saɓanin raáyi akan yarjejeniyar ba, dukkanin shugabanin sun nuna aniyar su ta cimma matsaya guda domin cigaban tarayyar turai.

Kamar dai kundin tsarin mulkin shima daftarin yarjejeniyar ya tanadi samar da manufar harkokin waje na bai ɗaya na tarayyar turai da kuma samar da shugaba na dundundun domin maye gurbin shugabancin karɓa karɓa na watanni shida da kan zagaya a tsakanin ƙasashen 27 na tarayyar turai. Bugu da ƙari za kuma a sauƙaƙa ayyuka da yawan dogon turanci wajen zartar da shawarwari.