1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta albarkaci matakin jinkirta tattaunawar daukar Turkiya

December 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuXo

Shugabannin kasashen KTT sun amince kan cewar dole kasashen dake son shiga kungiyar nan gaba su cike dukkan tsauraran ka´idojin shiga kungiyar ta EU. To amma lokaci daya sun ce ba za´a samu wani sabon cikas ga fadada kungiyar ba. A lokacin taron kolin su na yini biyu a Brussels shugabannin kasashen 25 na kungiyar sun albarkaci matakan da aka dauka na dakatar da tattaunawar shigar da Turkiya cikin kungiya saboda kin da ta yi na bude tashoshin ruwanta ga Cyprus, wadda memba ce a EU. Ana kuma sa ran cewa taron zai tattauna akan yiwa hukumomin kungiyar ta EU kwakskwarima gabanin a fadada ta. Da farko SGJ Angela Merkel wadda kasar ta zata karbi shugabancin kungiyar a farkon sabuwar shekara ta ce idan ba´a amince da kundin tsarin mulkin EU kafin shekara ta 2009 ba, to hakan zai zama wata gazawa ta tarihi.