1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU da Majalisar shawara ta kasashen Turai

Mohammad Nasiru AwalAugust 10, 2004
https://p.dw.com/p/BvhR
Majalisar Shawara ta kasashen Turai a birnin Strassburg
Majalisar Shawara ta kasashen Turai a birnin Strassburg

Kirkiro majalisar shawara ta kasashen Turai a shekarar 1949 shine ya bude babin shirye-shiryen hade nahiyar Turai. A halin da ake cikin wannan majalisa na da membobi 45. Baya ga karamar kasar nan wato Monaco da Belarus, wadanda a halin yanzu ake tattauna batun daukarsu, dukkan kasashen wannan nahiya na da wakilci a wannan majalisa. Babbar manufar majalisar dai ita ce tabbatar da ´yancin dan Adam. Ga Mohammad Nasiru Auwal dauke da karin bayani game da takaddamar da ake yi tsakanin wannan majalisa da kuma kotun kolin kungiyar Tarayyar Turai game da hukumar da ta cancanci kula da batutuwan da suka shafi ´yancin dan Adam a Turai.

Ko shakka babu kundin tsarin mulki na da muhimmanci ga kungiyar tarayyar Turai EU, inji Juliane Kokott babbar lauya a kotun kolin Turai dake Luxemburg. A cikin wannan tsarin mulki kuwa an yi batu game da ´yancin dan Adam, inji lauyar sannan sai ta kara da cewa.

"Abin tambaya dai shine yadda za´a aiwatar da batun na ´yancin dan Adam. Har yanzu kuwa ba´a warware wannan batu ba. A halin da ake ciki hukumomi guda 3 a cikin kungiyar EU ne ke kula da batun ´yancin dan Adam, wato kotunan kasa da kotun Turai mai kula da batutuwan da suka jibanci ´yancin dan Adam sai kuma kotun kolin kungiyar gamayyar Turai. Hakan dai ka iya janyo sabani a fannin shari´a."

Abin da ke a bayyane dai shine kawo yanzu kotun kolin majalisar shawara ta kasashen Turai ce ke akan kotun kasa a butuwan da suka shafi ´yancin dan Adam. Wato duk wanda bai amince da hukuncin kotun kasar sa ba, yana iya daukaka kara a gaban alkalai a birnin Straßburg. Wadanda hukuncin su ke akan na alkalan kotunan kasashen Turai.

Tambayar da ake yi yanzu ita ce wai shin mai zai faru idan aka fara aiki da sabon kundin tsarin mulkin kungiyar EU mai tattare da batutuwa na shari´a? Shin dole kenan ´ya´yan kungiyar su rika zuwa Luxemburg akan batutuwan da suka shafi ´yancin dan Adam? Ko kuma suna iya zaba tsakanin kotunan na EU da kuma majalisar shawara ta kasashen Turai? Ko kuma zasu iya daukaka kara a wata kotun idan hukuncin da daya kotun ta yanke bai gamsar da su ba?

Da alamu dai ba za´a kai ga wannan hali na dambarwar shari´ar ba. Domin tun yanzu majalisar shawara ta kasashen Turai da kungiyar EU sun amince da daukar matakan don hana shiga cikin wannan hali. Alal misali majalisar ce zata ci-gaba da kula da batutuwan da suka shafi ´yancin dan Adam wato kotun kungiyar EU a Luxemburg zata rika tura duk kararraki game da ´yancin dan Adam zuwa birnin Straßburg.

Tuni kuwa an yi tanadin yin haka a kundin tsarin mulkin, inda kungiyar EU a madadin dukkan kasashe membobinta zata sanya hannu akan yarjejeniyar kare hakin dan Adam, don bawa alkalan majalisar shawarar cikakken ikon tafiyar da aikin kula da batutuwan na ´yancin dan Adam. Hakan kuwa na da fa´idar gaske domin kotun ta birnin Straßburg na matsayin wata hukuma da babu ruwanta.