Kungiyar EU da Amirka na matsa lamba ga tura dakaru Darfur | Labarai | DW | 23.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU da Amirka na matsa lamba ga tura dakaru Darfur

Ministan harkokin wajen Faransa Philippe Douste-Blazy ya ce ministocin harkokin wajen Amirka da na KTT zasu aikaewa da wata tawaga zuwa Sudan da nufin shawo kan gwamnati ta amince da girke dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD a lardin Darfur. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta yi nuni da cewa lardin na yammacin Sudan na fuskantar munanan tashe tashen hankula. Ta fadawa ministocin dake taro a gefen babbar mashawartar MDD cewa sabon farmakin da dakarun Sudan ke kaiwa ´yan tawaye a Darfur ya hana kai dauki ga dubun dubatan ´yan gudun hijira. A ziyarar da ya kaiwa MDD cikin wannan mako shugaban Sudan Omar al-Bashir ya sake nuna adawa da maye gurbin dakarun kungiyar tarayyar Afirka da ba su da isassun kaya aiki da wata rundunar MDD.