1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 2, 2015

Wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne da ke gwagwarmaya da makamai a Tarayyar Najeriya, sun hallaka sama da mutane 100 a Arewa maso Gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/1Frwl
Hare-haren Boko Haram a Najeriya
Hare-haren Boko Haram a NajeriyaHoto: AFP/Getty Images/Stringer

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa maharan sun hallaka mutanen ne yayin da wasunsu ke sallah a masallatai wasu kuma ke yin girki a cikin gida. Lamarin dai ya afku ne a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar da ke zama tushen kungiyar ta Boko Haram.

Wani shaidan gani da ido mai suna Kolo mazaunin kauyen Kukawa da kuma wani masunci sun tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da afkuwar lamarin.

Kungiyar Boko Haram ta kuma bindige wasu mutane 48 da ke sallah a masallaci har lahira tare da raunata wasu mutane 11 a wani harin na daban da ta kai jim kadan bayan da ta kai na farko.