Kungiyar AU da NATO | Siyasa | DW | 17.05.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kungiyar AU da NATO

Kungiyar Tarayyar Afurka AU na bukatar taimako daga kungiyar NATO domin tafiyar da ayyukan tsaron zaman lafiya Darfur

Alpha Konare da Gerhard Schröder

Alpha Konare da Gerhard Schröder

An dai saurara daga bakin sakatare-janar na kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika ta NATO Jopp de Hoop Scheffer yana mai bayani a fili cewar kungiyar ba ta sha’awar zama wata ‚yar sandan duniya. Wannan bayanin na nufi ke nan cewar kungiyar zata yi shisshigi a rikicin Sudan ne bisa wasu tsayayyun sharudda. Musamman ma na cewar ba zata shigar da mayakanta a rikicin ba. Wannan alhaki ne da ya rayata akan su kansu kasashen Afurka, kamar yadda aka ji daga bakin wakilin kungiyar tarayyar Afurkan Alpha Konare a Brussels. Kungiyar ta lashi takobin cewar zata yi bakin kokarinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lardin Darfur mai fama da rikici a yammacin Sudan, inda take da niyyar tura sojojin kiyaye zaman lafiya dubu biyar zuwa dubu takwas, in ji Alpha Konare, wanda ya kara da cewar:

Rundunar da za a tura zuwa Darfur ta kunshi sojojin Afurka ne su ya su. Ina mai tabbatar muku da cewar ba za a samu sojan wata kasa ta ketare, in banda sojojin Afurka su ya su a lardin Dafur ba.

To sai dai kuma kungiyar ta tarayyar Afurka tana da wata ‚yar bukata. Kungiyar tana fama da karancin kayan aiki. Tana bukatar taimako wajen jigilar sojojin nata da yi musu muhallin zama da ba su isasshen horon da ya dace da kuma kyautata ayyukansu na sadarwa, a wannan bangaren kungiyar NATO na iya taimakawa gwargwadon ikonta. Sakatare-janar na kungiyar ta NATO Joop de Hoop Scheffer ya nuna yiwuwar ba da irin wannan goyan baya, bayan da illahirin kasashenta suka amince da haka. Tun da farkon fari dai kasar Sudan ta bayyana kyamar ganin tsoma hannun kungiyar NATO a wannan mataki na tsaron zaman lafiyar Darfur. Kazalika hatta a tsakanin kasashen kungiyar ta tsaron arewacin tekun atlantika akwai masu adawa da matakin. Kasar Faransa sai da ta nunar a fili cewar zata fi sha’awar ganin an gabatar da wani mataki a karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Turai. A farkon wannan watan kasar ta Faransa ta nuna yiwuwar samun taimakon jigilar sojojin da kuma ba su horo daga Kungiyar tarayyar Turai. Alpha Konare dai ya ce ba wani mataki ne na hadin guiwa ake neman dauka tsakanin kungiyar tarayyar Afurka da ta tsaron arewacin tekun atlantika NATO ba. Su ma sauran kungiyoyin suna iya ba da gudummawa gwargwadon ikonsu. An ji irin wannan bayanin daga Joop de Hoop Scheffer, sakatare-janar na kungiyar NATO. A halin da muke ciki yanzu haka kungiyar tarayyar Turai ta ba da taimakon abin da ya kai Euro miliyan 500 domin sassauta radadin mawuyacin halin da talakawa ke ciki a lardin Darfur. Akwai kuma kwararrunta akan al’amuran tsaro da ta tura zuwa Darfur yanzu haka. An kiyasce cewar dubban mutane ke mutuwa a wannan lardin a kowane wata, a baya ga wasu miliyoyin dake ciki hali na zautuwa. Akalla dai sassan da basa ga maciji da juna a rikicin lardin suna kokarin kyautata makomar shawarwarinsu na cimma zaman lafiya.