Kungiyar Amnesty ta yi tur da tsare mutane a Iraqi ba tare da sharia ba.
March 6, 2006Talla
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Amnesty International ta yi Allah wadai da tsare mutane da yawan su ya kai 14,000 a gidan kurkuku a kasar Iraqi ba tare da an yi musu shariá ba. Kungiyar na mai cewa har yanzu hukumomi basu hankalta ba daga abun kunyan nan na tabargazar wulakanta jamaá a gidan yarin Abu Ghuraib. Daraktan Kungiyar ta Amnesty Kate Allen ta baiyana cewa matukar sojojin Amurka da Britaniya za su cigaba da tsare mutane a gidajen kurkuku na sirri , to kuwa zaá cigaba da fuskantar tozartarwa da cin zarafin bayan Allan da ake tsare da su. Kungiyar ta Amnesty ta yi kira da a kawo karshen tsare mutanen wanda ta baiyana da cewa ya keta dokokin kasa da kasa.