Kungiyar Amnesty ta dorawa isra´ila laifin mutuwar Falasdinawa a bakin tekun Gaza | Labarai | DW | 14.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Amnesty ta dorawa isra´ila laifin mutuwar Falasdinawa a bakin tekun Gaza

Sabanin bayanan da Isra´ila ta bayar, wani bincike da kungiyar kare hakin bil Adama ta Human Rights Watch ta yi ya dorawa Isra´ila laifin mutuwar wasu fararen hula 8 a gabar tekun Gaza. Kwararen masanin aikin soji na kungiyar, Marc Garlasco ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP a yau laraba cewa birbishin karafan da suka gano a wurin da aka kai harin da kuma raunukan da wadanda wannan abu ya rutsa da su suka samu bai bar wani shakku ba cewa wani gurnati ne ya fashe. A jiya talata gwamnatin Isra´ila ta ce binciken da ta yi ya gano cewa wata nakiyar karkashin kasa ce ta fashe a gabar tekun. To sai dai ba kamar Garlasco ba, Isra´ila ba ta nunar da cewa ta gudanar da binciken a wurin da makamin yayi bindiga ba, illa iyaka binciken na ta ya dogara akan hotunan telebijin da kuma bayanan na hukumar leken asiri. Duk da haka jakadanta a MDD Dan Gillermann ya goyi da bayan gwamnatinsa.