Kungiyar Alkalai a Nijar ta nemi minista ya yi murabus
February 25, 2017Talla
A Jamhuriyar Nijar a ranar Asabar nan ne hadadiyar kungiyar alkalai ta kasar ta kira wani taron manema labarai inda a ciki ta bukaci ministan kudin kasar Hassoumi Masasoudou da ya yi murabus ya kuma gurfana a gaban kuliya domin wanke kansa bisa zarge-zargen da a ke masa na cewar ya na da hannu a cikin badakalar salwantar makuddan kudade kimanin miliyan dubu 200 a cikin wani asusun ajiya a kasar Dubai.A farkon makon jiya ne dai wata jarida mai zaman kanta ta ambaci badakalar tare da ambata sunan ministan da hannu dumu-dumu a cikin zargin da ministan ya karyata ya na mai cewar shaci fadi ce kawai irin ta 'yan jarida,