Kun san ko waye Martin Schulz? | Zaben Jamus 2017 | DW | 21.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zaben Jamus

Kun san ko waye Martin Schulz?

Martin Schulz na jam'iyyar SPD guda ne daga cikin fitattun 'yan siyasar Jamus wanda a halin yanzu ya ke zawarcin kuri'un al'ummar kasar don zama shugaban gwamnati.

"Ina son in zama shugaban gwamnati", wannan shi ne kalaman Martin Schulz dan takarar neman shugabancin Jamus karkashin jam'iyyar SPD. Wai shin zai iya cimma wannan buri? Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta sanya shugabar gwamnati Angela Merkel ta jam'iyyar CDU gaba amma Schulz ya ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Shi dai Martin Schulz mai shekaru 61 dan asalin wani karamin gari ne da ake kira Würselen da ke kusa da birnin Aachen a nan jihar NRW. Burinsa na zama dan wasan kwallon kafa ya hana shi kammala makaranta amma kuma burin bai cika sakamakon raunin da ya yi ya na dan shekara 17 a duniya. A wata hira da aka yi da shi, Schulz ya ya ce "na bar makaranta, na sha fadi tashi a rayuwata amma duk da haka ina alfahari da irin abubuwan da na cimma a rayuwa kawo yanzu.

Deutschland wählt BTW-Reise ARD-Wahlarena Schulz SPD (DW/R. Oberhammer )

Schulz guda ne daga cikin 'yan siyasar Jamus da suka yi fice a nahiyar Turai

"

Daga baya ya bude shagon sayar da littafi a garin na Würselen kafin daga bisani ya shiga harkokin siyasa. Ya na da shekara 31 aka zabe shi mukamin magajin garin Würselen sannan a shekara 1994 ya ci zaben dan majalisar dokokin Turai inda ya zama shugabanta a 2012. Kwarewarsa kwararre a fannin siyasar Turai ta taimaka wa Schulz mai aure da 'ya'ya biyu ya samun saukin dawowa gida don shiga siyasar kasarsa, inda da gagarumin rinjaye nasarar babban taron jam'iyyar SPD ya tsayar da shi a matsayin dan takararta a zaben neman mukamin shugaban gwamnatin Jamus na 2017 bayan da shugaban SPD Sigmar Gabriel ya ki tsayawa.

Shekarar zaben 2017 ta fara masa da kyau domin da yawa daga cikin 'ya'yan jam'iyyar na yi masa kallo mai ceto wanda shi kadai ne zai iya kada shugabar gwamnati Angela Merkel kuma a farkon shekara kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nunar da haka sai dai daga bisani an koma gidan jiya wato SPD ta yi kasa kamar yadda shi da kanshi ya shaidar har ma ya ke cewar "ni ma ina karanta sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a sai dai duk kuri'ar jin ra'ayin jama'a na da abu iri daya wato kusan rabin masu zabe a nan kasar ba su yanke hukuncin wanda za su jefa wa kuri'a ba. Hakan ke sa yakin neman ya yi armashi. Saboda haka na dukufa yanzun wajen neman kuri'un wadanda ba su yanke hukunci ba tukuna kuma da na samu zan ci zaben majalisar dokokin tarayya. Wannan shi ne burina."

Deutschland wählt BTW-Reise ARD-Wahlarena Schulz SPD (DW/R. Oberhammer )

Zawarcin kuri'un wanda ba su yanke hukuncin wanda za su zaba ba na daga cikin dabarun Schulz na cin zabe

Daya daya cikin batutuwan da ke daukar hankali a zaben na bana shi ne yadda za a dakile kwararar 'yan gudun hijira musamman daga kasashen Afirka zuwa Jamus. A hira ta musamman da DW ta yi da shi a karshen mako, Martin Schulz ya ce zai hada kai da shugabannin kasashen irinsu Nijar don gano mafita inda ya ce "muna son mu kawo karshen fitaucin dan Adam, muna yin aiki tare da kasashen irinsu Nijar da dai sauransu. Hakan zai yiwu ne kawai karkashin sa idon kungiyoyi na kasa da kasa, domin dole a mutunta dokoki kundin tsarin mulki, akwai kuma barazanar cewa wasu kasashen ba za su iya yin biyaya da ka'idojin kasa da kasa ba."