Kudurin Sassauci kan hukuncin kisa | Labarai | DW | 19.12.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kudurin Sassauci kan hukuncin kisa

Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da bana tilas ba ,dake kira dangane da sassauci kann aiwatar da hukuncin kisa.An cimma wannan kuduri ne bayan kada kuria,inda kasashe 104 suka amince kana 54 suka yi adawa,ayayinda wasu 29 suka ki bayyana.Italiya , a madadin kungiyar tarayyar turai Eu,ta amince da wannan kuduri.Ayayinda Amurka da Masar da Iran da mafi yawa daga cikin kasashen Asia ,sun kada kuri’un adawa da hakan.Rahotan kungiyar kare hakkin jamaa ta Amnesty International ya nunar dacewa,kasashen China da Iran Da Iraki da Amurka da Pakistan da Sudan ,sune ke dauke da alhakin kashin 90 daga cikin 100 na yawan kisan gilla da akeyi a duniya.

 • Kwanan wata 19.12.2007
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Cdiz
 • Kwanan wata 19.12.2007
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Cdiz