kudurin komitin sulhu kan Darfur | Labarai | DW | 01.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

kudurin komitin sulhu kan Darfur

Komitin sulhun mdd ta amincewa mdd ta karbi harkokin kiyaye zaman lafiya a lardin darfur dake yammacin Sudan,wanda ke zama dada tursasawa gwamnatin Khartum,bukatar dakatar da adawa datake cigaba da hakan.

!2 daga cikin wakilan komitin 15 ne suka kada kuriar amincewa da kudurin tura dakarun mdd Darfur din,wanda ke bayyana cewa tura dakaru dubu 17,300 na mdd zai taimaka matuka gaya a lardin,amma bisa ga amincewan gwamnatin na Sudan.

Kasashe 3 masu wakilci,Sin da Rasha da Qatar,sunki halartan zaman kada kuriar raba gardamar ta komitin.Hakan dai na nufin cewa,a halin yanzu dakarun kiyaye zaman lafiyan mdd zasu maye gurbin sojin kiyaye zaman lafiya na kasashen Afrika,wadanda a halin yanzu ke fama da karancin kayan aiki a Sudan din,kuma suka gaza kawo karshen rigingimun dake cigaba da addabar yammacin wannan kasa.Jakadan Amurka John Bolton yace,wannan yarjejeniya da aka cimma na bukatar daukar matakai na gaggawa,domin ceto mutanen Darfur.Ita kuwa gwamnatin Sudan din cewa tayi,wannan zartarwa bashi da wata hujja balle makama.

 • Kwanan wata 01.09.2006
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5e
 • Kwanan wata 01.09.2006
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5e