Kuduri akan ′yan gudun hijira a nahiyar Turai | Siyasa | DW | 05.02.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kuduri akan 'yan gudun hijira a nahiyar Turai

Turai na kokarin kalubalantar matsalolin 'yan gudun hijira

default

A yau ne 'yan majalisar Turai ke mahawarar zartar da kuduri akan cibiyoyin 'yan gudun hijira a nahiyar Turai.Wannan dai bazai kasa nasaba da nazarin da marubuciyar majalisar turan tayi kan hali mawuyaci da 'yan gudun hijiran ke ciki ba.

Martine Roure ta ce 'yan gudun hijiran na cikin hali mawuyaci na rayuwa tare da kira da bukatar zuwa ziyartar cibiyoyin da samarda tsari guda a nahiyar turan. Mai sassaucin ra'ayin kuma 'yar kasar faransa, ta nuna goyon bayanta wa ƙasashen yankin kudanci da kuma gabashin turai, dangane da adawa da suke da kamfaign da akeyi kan 'yan gudun hijiran.

Miliyoyin mutane dai na yiwa turai hangen aljannar duniya, inda kowa ke fatan zuwa. Batu daya kasance babbar matsala wa majalisar turan na kalubalanta a kasashe kimanin 11 na nahiyar dake fama da kwararan 'yan gudun hijira.

Akwai matsaloli dai na rashin tsabta a sansanonin,kana ga matsaloli na rashin lafiya da samun magunguna.

Martine Roure dake zama mataimakiyar shugaban majalisar Turan ta yi karin haske dangane da halin da 'yan gudun hijiran ke ciki..

Martine Roure und Patrick Gaubert EU Abgeordnete

Martine Roure

"A yawancin lokuta zaka ga cewar basu da mutanen da zasu taimaka musu sanin abunda zasu yi. Wannan shine matsala ta farko, kana mafi yawa daga cikin waɗannan mutanen hankalinsu ya rikiɗe. A takaice kashi daya daga cikin uku kaɗai na ƙasashen da sansanoni ne kawai suke iya biyan bukatun 'yan gudun hijiran dangane da batutuwa da suka shafi rashin lafiya da magunguna"

Wasu ƙasashen dake nahiyar turan dai suna da saɓanin ra'ayi dangane da yadda wasu ke karɓa da kuma kula da 'yan gudun hijiran ninji mataimakiyar shugaban majalisar. Sai dai batun ya shafi dukkannin ƙasashen kudanci da gabashin nahiyar ne inda ana ne ake da mafi yawan 'yan gudun hijiran,kamar ƙasar Girka.

Saboda inda ƙasar Girkan take dai ,ta kasance inda mafi yawan 'yan ƙasashen Asia ke zuwa.Sansanin 'yan gudun hijiran dake garin Ostägäis dai sun cika fiye da kima. Wakilin Girka a Majalisar Turai Loannis Varvitsiotis ya bayyana cewar shekaru biyun da suka gabata ne aka buɗe wani sansanin 'yan gudin hijira na zamani a tsibirin Samos..

Flüchtlinge brechen aus Lager auf Lampedusa aus

Tsibirin Lampedusa

"Yace gaskiya ne, ada dai waɗannan sansanonin 'yan gudun hijira, akwai dukkan abubuwan da mutane ke bukata. Amma a yanzu muna ganin matsaloli sun fara yin yawa. Sabbin gine gine da dukkannin abubuwa da ake bukata,har ma da Likitoci da zasu kula da baƙin dake kwararowa"

Kazalika haka matsalar take a Italiya.A tsibirin Lampedusa ,akwai bcunkoson 'yan gudun hijira sama da 1200 a wuri guda dake jiran tsammani, wurin daya kamata zai dauki mutane 800.

Gwamnatin Italiyan dai ta sanar da bukatar ɗaukin gaggawa wa 'yan gudun hijiran, tare da gabatar da halin da take ciki wa kungiyar ta EU. Giusto Catania shine wakilin kasar Italiya a majalisar ...

" yace gwamnatin kasar Italiya ce ta sanar da wannan dokar ta ɓaci, sa'annan ta gabatar Turai wannan shiri saboda batason karɓan 'yan gudun hijiran tsibirin Lampedusa kai tsaye. Saboda kashi 75 daga cikin 100 na 'yan gudun hijiran Lampedusan,masu neman mafakar siyasa ne"