Kudirin tsagaita wuta a Lebanon ya fara aiki | Labarai | DW | 14.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kudirin tsagaita wuta a Lebanon ya fara aiki

Shirin tsagaita wuta a kasar Lebanon ya fara aiki bisa cimma yarjejeniya da kuma tsoma baki da majalisar dinkin duniya ta yi na kawo karshen wata guda cur da aka yi ana bata kashi tsakanin sojojin Israila da dakarun Hizbullah. Kudirin tsagaita wutar na Majalisar dinkin duniya ya yi kiran dakatar da dukkanin farmaki tare kuma da tura sojoji 15,000 na Majalisar dinkin duniya wadanda za su sa ido domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya. Bugu da kari kudirin ya bukaci tura karin sojoji 15,000 na gwamnatin Lebanon zuwa kudancin kasar yankin da dakarun Hitzbullah suke domin sa ido a kan su. Yarjejeniyar ta bukaci Israila ta janye sojojin ta 30,000 wadanda ta jibge a kudancin Lebanon. A daren jiya bangarorin biyu sun yi musayar wuta gabanin cikar waadin tsagaita wutar. An ruwaito cewa Israila ta yi luguden wuta a yankunan gabashin Lebanon da kuma kudancin birnin Sidon inda suka yi ta dauki ba dadi da dakarun Hizbullah. Bangarorin biyu sun ce za su maida martani idan daya bangaren ya karya yarjejeniyar tsagaita wutan. Yakin dai ya barke ne bayan da Hizbullah ta yi garkuwa da sojoji biyu na Israila a tsakiyar watan Yulin da ya gabata.