1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kudirin Majalisar dokokin Amurka a game da kisan Armeniyawa a Turkiya

Kwamitin Majalisar dokokin Amurka ya amince da daftarin ƙudiri cewa kisan da aka yiwa Armeniyawa a ƙasar Turkiya a zamanin mulkin Usmaniya a shekarar 1915 kisa ne na ƙare dangi. Kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin ya zartar da ƙudirin duk da kashedin da fadar gwamnati ta White house ta yi cewa hakan na iya shafar dangantakar Amurkan da ƙasar Turkiya. Turkiya babbar aminiya ce ga ƙungiyar tsaro ta NATO da kuma Amurka a yaƙin da take a Iraqi. Ƙudirin wanda bai zama tilas a aiwatar da shi ba, zaá gabatar shi a zauren majalisar domin kaɗa ƙuriá. Shugaban ƙasar Turkiya Abdullahi Gul ya baiyana shawarar kwamitin majalisar dokokin da cewa ba mai karɓuwa bane. Turkiyan dai ta yi watsi da zargin cewa an yiwa Armeniyawa kimanin miliyan ɗaya da rabi kisan gilla a lokacin yaƙin duniya na ɗaya a zamanin daular Usmaniya.