Kudirin karni na MDG | Siyasa | DW | 11.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kudirin karni na MDG

Anya za'a cimma kudirin karni na MDG nan da shekara ta 2015 kuwa ?

default

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan

A ranar 20 zuwa 22 ga wannan watan na Satumba ne za'a gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya wanda zai sami halartar shugabannin kasashe domin tattaunawa akan shin ko akwai yiwuwar cimma kudirin karni na MDG nan da shekara ta 2015 ? kuma ta wace hanya za'a cimma wannan buri ?. Akan haka ne a ranar Juma'ar da ta gabata shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ke daya daga cikin mahalarta taron ta tattauna da tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan tare da sauran masana a birnin Berlin.

A yanzu dai shekaru biyar suka rage domin kaiwa ga kudirin karnin na Millenium Development Goal da aka debarwa wa'adin shekaru goma sha biyar domin cimma dukkanin kudirori takwas da aka zayyana a karkashin wannan shiri. Karamin rahoton da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya gabatar a kwanan nan ya baiyana karara cewa wadannan shekaru biyar da suka rage ba zasu isa a cimma dukkanin wadannan kudirori ba. Yace ko da yake akwai cigaba da kuma nasarori da aka samu wajen yaki da cutar AIDS dana zazzabin cizon sauro wato Malaria da kuma yunkurin da ake yi na samar da ruwan sha mai tsabta ga al'uma, a bangare guda kuma akwai kalubale da ake fuskanta. Alal misali yadda aka sami karuwar mutane dake fama da yunwa maimakon a ce sun ragu. Tsohon sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan yace akwai sauran aiki a gaba.

Kinder im Aids Hospiz in Addis Abeba

Asibitin kula da yara a Addis Ababa, daya daga cikin kudirorin karni na MDG

" Hakika idan shugabannin suka hadu a mako mai zuwa, akwai bukatar su duba hanyoyin hanzarta cimma wanna kudiri yadda kasashe da dama za su sami damar cimma kudirorin cikin shekaru biyar masu zuwa, amma idan basu yi hakan ba, to kuwa bai kamata su tsaya a nan ba domin kudirorin suna da muhimmanci, a saboda haka sai su cigaba da lalubo hanyoyi yadda za su aiwatar da wadannan manufofi har ya zuwa bayan shekarar 2015".

Wannan ita ce shawarar da shima sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban  Ki-Moon ya bayar, samar da wata manufa da za'a cigaba da aiwatar da wadannan manufofi da aka sanya a gaba. A nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kira ta yi a aiwatar da gagarumin sauyin manufa domin cimma wannan kudiri.

A waje guda dai bayanai sun nuna cewa a shekaru goma da suka wuce tallafin da manyan kasashe ke baiwa kasashe matalauta basu wadatar ba. Musamman ma dai manyan kasashen sun gaza a alkawuran da suka daukarwa kansu na ware wasu kudade a matsayin gudunmawar jin kai ga kasashe matalauta domin cimma wannan kudiri. Daga cikin wadannan kasashe kuwa har da Jamus wadda a maimakon 0.51 cikin dari na abin da take samarwa a shekara da ta yi alakwarin  bayarwa a matsayin gudunmawa, 0.4 kawai take bayarwa. Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel wadda zata halarci taron muhawara kan tallafin kudin a birnin New York ta ce batun karin gudunmawa ma bata taso ba.

" Babu shakka batun kudi na da muhimmanci kuma na sha baiyanawa cewa Jamus za ta cigaba da bada gudnmawarta duk da matsin tattalin arziki da ake ciki, ba za mu rage ko da sisin kwabo daga cikin abinda muke bayarwa ba. Amma kuma akwai bukatar duba yadda ake amfani da kudaden, hakan kuwa zai samu ne ta hanyar hadin  gwiwa tsakanin kasashe masu bada gudunmawar da kuma kasashen da ake tallafawa".

Mawallafa : Nina Werkhäuser / Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu