Kotunan musulunci a Somalia sun zargi Ethiopia da kai hare haren cikin ƙasar | Labarai | DW | 19.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotunan musulunci a Somalia sun zargi Ethiopia da kai hare haren cikin ƙasar

Shugabanin Kotunan musulunci a Somalia, da ke riƙe da Mogadiscio babban birnin ƙasar, da ma wassu sassan, sun zargi dakarun ƙasar Ethiopia, da kai hare hare ga Somalia.

Sun kuma yi barazanar maida martani.

A yayin da ya ke tsokaci ga wannan batu ,kakakin gwamnatin riƙwan ƙwaryar Somalia, Abdurahman Nur Mohamed Dinari, ya mussanta wannan zargi.

Ya ce kawai, dakarun kotunan musulunci, na buƙatar ƙirƙiro wani dalilin kai hari ,ga birnin Baidowa, dake kusa da iyaka da Ethiopia, wanda kuma a halin yanzu, ke matsayin cibiyar gwamnatin riƙwan ƙwarya, da a ka girka, tun shekara ta 2004.

Kakakin ya ƙara da cewa, dakarun su, a shire su ke, su kare Baidowa daga duk wata barazana.

Wannan saban yanayi, na ƙara tsunduma al´ummar Somalia, cikin zullumin massifar yaƙi, da ya ta ka faɗa tun shekara ta 1991.

Itama gwamnatin Addis Ababa, ta mussanta zargin, da cewar bai da tushe bare makama.

Sannan shugaban hukumar kulla da yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ya gayyaci ɓangarori daban-daban masu yaƙar juna a Somalia, zuwa taron sulhu.