Kotunan Islama a Somalia ta zargi Ethiopia da tura sojoji cikin kasar | Labarai | DW | 17.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotunan Islama a Somalia ta zargi Ethiopia da tura sojoji cikin kasar

Mayakan kotunan Islama a Somalia sun ce sojojin Ethiopia wato Habasha kimanin 300 sun kutsa cikin kasar makwabciyar Ethiopia. Shugaban kungiyar kotunan Islama Sharif Sheikh Ahmed ya fadawa manema labarai cewa da sanyin safiyar yau sojojin sun tsallake kan iyakar Dollow dake kudu maso yammacin kasar. Shugaban kotunan ya zargi Amirka da marawa sojojin Ethiopian da suka shiga kasar sa baya. Kawo yanzu Ethiopia ta musanta cewar sojojin ta sun kutsa cikin Somalia. A jiya dubun dubatan magoya bayan sojojin sa kai na Islama, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Mogadishu don nuna adawa da tura dakarun ketare zuwa kasar. Zanga-zangar ta zo ne a daidai lokacin da ´yan Islaman suka kara karfafa ikon su a daukacin kudancin Somalia, bayan sun karbe yankunan daga kawancen madugan yaki dake samun goyon bayan Amirka.