Kotun Sojin Amirka a Guatanamo ta yi watsi da tuhumar firsinoni biyu | Labarai | DW | 05.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Sojin Amirka a Guatanamo ta yi watsi da tuhumar firsinoni biyu

Wata kotun sojin Amirka a sansanin Guatanamo ta yi watsi da caje cajen da aka yiwa wani dan Kanada da kuma wani dan Yemen. Kotuin sojin ta Amirka ta zargi Omar Khadir dan Kanada da kisan sojin Amirka daya a wani harin gurnati lokacin wani samame da sojin Amirka suka kai kan ´yan Al-Qaida a Afghanistan shekaru 5 da suka wuce. To amma alkali ya ce ba ya da wani zabi face yayi watsi da tuhumar domin ba´a ayyana Khadir a matsayin wani haramtaccen soja ne abokin gaba ba. Wani kakakin ma´aikatar tsaron Amirka ya ce an janye tuhumar da ake yiwa dan kasar Yemen Salim Ahmed Hamdan wanda ya kasance mai tsaron lafiya Osama Bin Laden.