1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Nijar ta wanke Gamatie daga zargi

Mahaman Kanta MAB
July 13, 2017

Dan kungiyar farar hula Mahamadou Gamatie da aka tsare a kukurku a game da zargin bayyana kalaman da ka iya tunzira jama'a ya tsira bayan da kotu ta wankeshi. Sai dai ta yi wa wani dan siyasa na Lumana sakin talala .

https://p.dw.com/p/2gTev
Verfassungsgericht in Niamey Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Kotun da ke birnin Yamai ta cika makil da magoya bayan kungiyoyin farar hula da kuma na jam'iyyar Lumana da ke adawa domin shaidar da sakamakon shari'ar. Hukuncin ya tanadi sakin Mahamadou Gamatie wani jigo a kungiyar farar hula da ke da rajin kare hakkin dan Adam ta Alternative Espace Citoyen bayan da kotun ta wankeshi daga laifin tunzura jama'a ga yin bore. A yayin da Ibrahim Bana wani jigo a reshen matasa na jam'iyyar LUMANA AFRIKA ta Hama Amadou da ke adawa ya samu hukuncin daurin watanni uku wato daya a gidan yari, sauran biyun kuma a waje a matsayin sakin talala.

Sai dai lawyansu ya nuna mamaki dangane da hukuncin da aka yanke wa Ibrahim Bana saboda a cewarsa babu tabbacin cewa kalaman da ya wallafa a Facebook zai iya yin tasirin a kan al'umma a Nijar. Sai dai P H K Aboubakar da ke goyon bayan jam'iyyar Lumana ya nuna gamsasu da shari'ar, saboda a cewarsa alkalai sun kwatanta adalci.

Makonni biyun da suka wace ne aka kama wadanda aka yanke wa hukuncin. Sai dai kuma dan siyasa Bana bai tabbatar da ko zai daukaka kara koko a'a ba.