1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun MDD ta fara sauron karar kisan kiyashi a Bosnia

February 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6d
Hoto: AP

A yau kotun kasa da kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya dake shariár manyan laifukan yaki zata fara sauraron karar da kasar Bosnia ta gabatar inda ta ke tuhumar Serbia Montenegro da kisan kare dangi . Kimanin shekaru 13 da suka gabata, kasar ta Bosnia ta gabatar da karar ga kotun majalisar dinkin duniya inda ta ke bin kadin kisan gillar da Sabiyawa suka yiwa musulmi a lokacin yakin da ya wakana a tsakanin shekarun 1992 zuwa 1995 wanda aka yiwa musulmi kimanin 200,000 kisan gilla. Manazarta na baiyana cewa Bosnia zata fuskanci gagarumin kalubale a yayin gabatar da bayanan saboda akasarin bayanan cin zarafin sojojin Bosnia ne suka tsara shi. A hukumance Kasar Sabiya bata shiga yakin ba kaín da naín amma akwai hujjoji dake gaban kotun majalisar dinkin duniyar wadanda suka nuna Sabiya ta marawa mahukuntan Belgrade baya a lokacin wannan yakin. Ana sa ran lauyoyin Bosnia zasu maida hankali ne akan bayanan da aka tattara da suka jibanci tuhumar da aka yiwa tsohuwar gwamnatin Yugoslavia musamman kisan gillar da sojojin sabiya suka yiwa musulmi kimanin 8,000 a garin Srebrenica a shekarar 1995.