Kotun Majalisar Dinkin Dunia ta yi belin Jannar Sefer Halilovic
November 16, 2005Talla
Kotun kasa da kasa, ta Majalisar Dinkin Dunia da ke shari´ar manyan leffika, ta yi belin Jannar Sefer Halilovic, tsofan shugabna runduna tsaro ta Bosnia, da a ka tuhuma da hannu a cikin kissan kiyasun da ya wakana, a shekara ta 1993 a Bosnia.
Shugaban alkallan kotun ya wanke Jannar Halilovic, tare da cewa babu issasun hujoji ma su tabatar da miwan sa, a cikin kissan kiyasun.
Wandfa su ka shighar da karan sun zarge shi da hallaka mutane fiye da 60 a garuruwan Grabovica da Uzdol.
An tsare shi a wannan kotu, tun watan desember na shekara ta 2001.