1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun kolin Jamus ta goyi bayan gudanar da zabe na gaba da wa'adi

August 25, 2005

A hukuncin da ta yanke ranar alhamis kotun koli ta Jamus ta tabbatar da shawarar shugaban gwamnati Gerhard Schröder domin rushe majalisar dokoki da gudanar da zabe na gaba da wa'adi

https://p.dw.com/p/BvaD
alkalan kotun koli ta Jamus
alkalan kotun koli ta JamusHoto: AP

Shugaban gwamnati Gerhard Schrödrer bai yi wata-wata ba wajen yin madalla da zartaswar kotun kolin dake garin Karlsruhe, inda ya ce alkalan kotun daidai da shugaban kasa Horst Kohler sun kara tabbatar da ra’ayinsa. Zaben na gaba da wa’adi a ranar 18 ga watan satumba mai kamawa abu ne da ya zama wajibi a gudanar da shi, in ji Schröder, wanda a ganinsa gwamnatinsa ba ta da karfin ikon zartaswa kuma a sakamakon haka a ranar daya ga watan yulin da ya wuce ya gabatar da rokon rashin amanna da gwamnatinsa a majalisar dokoki ta Bundestag. A lokacin da yake jawabi Schröder karawa yayi da cewar:

Muhimmin abu a gare ni shi ne samun cikakken goyan baya ga manufofi na na garambawul, wadanda zasu taimaka Jamus ta sake samun karfafuwar matsayinta ba tare da an yi fatali da tsarinta na jin dadin rayuwar jama’a ba. A sakamakon haka nike bukatar wani sabon wa’adi na mulki, kuma zan ci gaba da gwagwarmaya akan haka a matsayina na shugaban jam’iyyar SPD.

Shi ma shugaban kasa Horst Köhler, wanda ya goyi bayan shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya kuma rushe majalisar dokoki ta Bundestag a ranar 21 ga watan yulin da ya gabata ya bayyana ra’ayinsa game da hukuncin kotun kolin, inda yayi kira ga jam’iyyun siyasa da su shiga yakin neman zaben tsakani da Allah sannan ya ce wajibi ne su kuma al’umar kasa su yi amfani da hakkinsu na zabe. Shugaban ya kara da cewar:

A yanzu masu zabe suna da cikakkiyar dama ta tsayar da shawara a game da alkiblar da suke bukatar kasarsu ta fuskanta nan gaba. A saboda haka nike gabatar da kira ga jama’a da su yi amfani da ‚yancinsu na kada kuri’a. Wannan ‚yanci ne dake da muhimmancin gaske.

A nasa bangaren ministan cikin gida Otto Schily cewa yayi, a yanzu babu sauran tababa a game da zaben na gaba da wa’adi tun da kotun koli ta albarkace shi. Dukkan jam’iyyun siyasar Jamus dai sun bayyana gamsuwarsu da zartaswar kotun kolin, wacce ta ba su damar kara karfafa damararsu ta yakin neman zaben na ranar 18 ga watan satumba mai kamawa. Tun da farkon fari dai ake sa ran samun irin wannan hukunci, amma ba wanda yayi zaton lamarin zai wakana akan irin wannan fasalin da babu tababa a cikinsa. Sai dai kuma a daya bangaren Werner Schulz dan jam’iyyar the Green dake daya daga cikin wadanda suka daukaka kara gaban kotun kolin ya bayyana rashin jin dadinsa da wannan hukuncin da ta zartas, wanda a ganisa yayi daura da manufofin mulkin demokradiyya. Kuma nan gaba shuagabannin gwamnati zasu rika yin koyi da irin wannan manufa domin rushe majalisun dokoki bisa ikirarin rashin gamsuwa da ikonsu na zartaswa.