kotun koli a Libya ta bada umurnin sake sauraron shariar wadanda suka sanyawa yara cutar kanjamu | Labarai | DW | 26.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kotun koli a Libya ta bada umurnin sake sauraron shariar wadanda suka sanyawa yara cutar kanjamu

Babbar kotun koli ta kasar Libya,ta bada umurnin a sake

sauraron shariar maaikatan jiyya nan 5 da wani likita Bapalasdine da aka yankewa hukuncin kisa bisa laifin sakawa daruruwan yaran Libya kwayar cutar HIV.

Shawarar da kotun ta yanke,ta baiwa masu laifin damar,sake baiyana matsayinsu gaban kotu,bayan shekaru 7 a gidan yari,b.

Maaikatan jiyya tuni suka baiyana cewa basu da laifi cikin wannan batu,inda suka ce an tilasta masu amsa wannan laifi ne.

Kwararru akan cutar kanjamau sunce,tuni HIV ta fara yaduwa a kasar Libya tun kafin zuwan wadannan maaikata,kuma akwai yiwuwar cutar ta yadu ne saboda rashin kyakyawar tsabta.