1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun kasa da kasa ta tabbatar da tsare ministan Rwanda

September 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuAp

Kotun kasa da kasa mai sauraron karrarkin laifukan yaki na Rwanda ta tabbatar da cewa an tsare tsohon ministan kasar da ake nema kann laifukan kisan kiyashi a Rwanda.A jiya laraba yan sandan Jamus suka tsare Augustine Ngirabatware a birnin Frankfurt inda yake boye.Tsohon ministan ana zarginsa ne da jagorantar tare da haddasa kisan kiyashi na Rwanda.Ana ganin Augustine shine ya bada makamai ga fararen hula da yan bindiga na kabilar Hutu a lokacin kisan kiyashi ba Rwanda inda akalla mutane 800,000 suka rasa rayukansu.