Kotun Isra´ila ta ce a sake hanyar ganuwar nan a Gabar Yammacin Kogin Jordan | Labarai | DW | 04.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Isra´ila ta ce a sake hanyar ganuwar nan a Gabar Yammacin Kogin Jordan

Kotun kolin Isra´ila ta yanke hukuncin cewa dole ne a canza hanyar da katangar nan ta Isra´ila zata ratsa a Gabar Yamma da Kogin Jordan. Alkalai a kotun sun amince da karar da Falasdinawa suka daukaka inda suka yanke hukunci cewa bai kamata katangar ta kawowa mazauna garin Bilin cikas ba wajen zuwa gonakin su. Kamar yadda Falasdinawa suka nunar, Isra´ila ta kwace filaye gonaki masu girma hekta 200 daga manoma inda ta sare dubban itatuwa na zaitun. A wani bincike da ta yi kimanin shekaru biyu da suka wuce kotun kasa da kasa a birnin The Hague ta bayyana wani bangare na katangar da cewa haratacce ne.