Kotun ICC tayi watsi da tuhumar da ake wa William Ruto | Labarai | DW | 06.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ICC tayi watsi da tuhumar da ake wa William Ruto

Kotun kasa da kasa da ke tuhumar masu tafka manyan laifuffuka ta ICC tayi watsi da zarge-zargen da ake yiwa mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto abisa rashin kwararan hujjoji.

Shi dai William Ruto gami da Joshua Sang da ke zama dan jarida an zarge sune da ruruta wutar rikicin kabilanci a inda mutane sama daubu dari suka hallaka sakamakon tarzomar zabubbukan kasar ta Kenya a shekara ta 2007.

Alkalan da ke a kotun ta birnin Hague ta kuma bayyana cewar babu sauran zarge-zarge a don haka sun rufe tuhumar da ake ma mutanen biyu, a inda ta kara da cewar wadanda suka shigar da karar suna kalubalantar su sun gaza kawo kwararan hujjoji

Tuni dai Joshua Sang da ke zama daya daga cikin wadanda ake tuhuma yayi wa Allah godiya tare da godewa al'ummar Kenyan baki daya.