1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC ta yankewa Charles Taylor hukuncin ɗaurin shekaru 50

May 30, 2012

Charles Taylor ya kasance tsofan shugaban ƙasa na farko da kotun ICC ta yankewa hukunci ɗauri dalili da ta'asar da ya tafka zamanin mulkinsa

https://p.dw.com/p/154aQ
epa03196470 Former Liberian President Charles Taylor takes notes as he waits for the start of a hearing to deliver verdict in the court room of the Special Court for Sierra Leone in Leidschendam, near The Hague, Netherlands, 26 April 2012. The UN-backed court was due to give a verdict in the trial of former Liberian president Charles Taylor, accused of 11 counts of crimes against humanity. The charges against him relate to alleged crimes in neighbouring Sierra Leone, where Taylor stands accused of arming rebels and masterminding grave human rights abuses during that country's war, which ended in 2002. EPA/PETER DEJONG/POOL
Charles TaylorHoto: picture-alliance/dpa

Daga shekara 1991 zuwa shekara ta 2002 ƙasar Sierra Leone ta fuskanci wani mummunan yaƙin basasa da ya yaɗu a wasu ƙasashen yankin yammacin Afrika.Bayan binciken da ta gudanar,kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta manyan lefikan yaƙi dake birnin Hague , ta ɗora alhakin wannan ta'asa ga tsofan shugaban ƙasar Liberiya Charles Taylor.

A wannan larabar, kotun ƙasa da ƙasa ta yanke masu hukuncin ɗaurin shekaru 50 a kurkuku game da wannan lefika.

Shekaru goma kenan da kawo ƙarshen yaƙin basasar da ya ɗaiɗaita ƙasar Sierra Leone da ma maƙwabciyarta Liberiya, to amma har yanzu jama'ar ƙasashen biyu na ɗauke da tabo ta fannoni daban daban, da gallazawar da suka yi fama da ita daga 'yan tawaye.Idrissa Tommy ganau ne ba jiyau ba, kuma yana daya daga cikin mutanen suka ɗanɗana azabar 'yan tawaye:'Yan tawayen sun cafke ni sun yi min dukar tsiya, mun kai mu shida a lokacin da suka kama mu haka kawai ,ba mu san hawa ba balle sauka

Wannan rikici ya ɓarke a Sierra a shekara 1991 a yayin da Charles Taylor tsofan shugaban ƙasar Liberiya, ya fara yin amfani da ƙananan yara cikin rundunonin yaƙi, a garurwuwan dake kan iyakokin Siera Leone da Liberiya da zumar samar da kuɗaɗen shimfiɗa mulki a ƙasar Liberiya.

In this picture released by the U.N., Former Liberian President Charles Taylor, center, bottom, is seen as he arrives at the airport in Monrovia, Liberia, Wednesday, March 29, 2006. U.N. peacekeepers escorted the former Liberian President Charles Taylor, in handcuffs, into jail Wednesday at the Sierra Leone tribunal where he is wanted for trial on war-crimes charges. (AP Photo/UN/ho) ** NO SALES **
cafke Charles TaylorHoto: picture-alliance/dpa

Wasu alƙalluma sun baiyana cewar harin da 'yan tayawen su ka ƙaddamar kan birnin Freetown na Siera Leone ranar shida ga watan Janairu na shekara 1999 ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu 40.

Jabati Mambu, wadda a lokacin ta na 'yar shekaru 15 a duniya ta ganewa idonta wannan masifa:Abinda sojojin tawayen ke yi shine su tattara yara matasa yuri guda su bindige su ɗaya bayan ɗaya.wani daga cikin dakarun tawayen da suka kama ni ya cilasta min ɗora hannuna ƙasa, daga nan take, ya datse min hannun da adda, nice ta farko sannan sauransu ka bi baya.

A shekara 2002 ne aka zo ƙarshen yaƙin ƙasar Siera Leone wanda Majalisar ɗinkin Duniya ta danganta da kasancewa ɗaya daga ta'asa mafi muni tun bayan yaƙin duniya na biyu.

Duk da cewar an share shekaru goma da kawo ƙarshen yaƙin, amma har yanzu illolin da suka biwo baya a fili suke, inji John Abu-Kwpaoh wani masanin tarihin:

Judges of the International Criminal Court Akua Kuenyehia, president Claude Jorda and Sylvia Steiner, top left to right, are seen at the start of a hearing in The Hague, Netherlands, Thursday, Nov. 9, 2006. The ICC opened a hearing to consider evidence against alleged Congolese warlord Thomas Lubanga, accused of recruiting child soldiers, a landmark first case for the permanent war crimes tribunal. Lubanga, the only suspect in the court's custody, is accused of recruiting child soldiers and using them to kill and mutilate his enemies. The hearing is meant to determine whether the evidence against Lubanga is strong enough to merit a full trial. ( AP Photo/ Bas Czerwinski)
Kotun ICCHoto: AP

"Mutane da yawa na raye da hannunko da ƙaffafu gustere.

Hukumar da aka girka domin tantance gaskiyar abinda ya faru ta tattaro baiyanai masu yawa, wasu ba daɗin ji.

Za ka ji yadda aka cilastawa mace ta yi jima´i da ɗanta na cikinta ko kuma wani muhharraminta.

A gaskiya duk tuhume-tumumen da ake yi Charles Tayor suna da tushe".

Dangane da duk wannan manyan lefikan na aikata ta'asa da kisan kiyasu gurfanar da Charles Taloyr gaban kotun kasa da kasa mai hukunta manyan lefikan ta birnin the Hague ko kuma la Haye, ya zama tamkar a ba gawa kashi don mai rai ya ji tsoro, inji Peter Andersen kakakin kotun ICC a birnin Freetown:Akasari a wannan yanki idan mutun na da ƙarfi babu wata kotu da za ta iya hukunta shi a wurin,saboda haka matakin da kotun The Hague ta ɗauka kan Charles Taylor ba ƙaramin cigaba ne ba, ta fannin wanzar da adalci.

Al'umar kasar Sierra mussamman wanda suka ukuba ga hanun 'yan tawayen sun nuna matukar farin cikin da hukuncin da kotun ICC ta yankewa Charles Taylor, ita Jabati Mambu bukata ma ta yi a yanke masu hukunci ɗaurin shekaru 150, ta yadda zai gama duk sauran rayuwarsa a kurkuku.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman