1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jean-Pierre Bemba ya kubuta daga kotun ICC

Salissou Boukari MNA
June 8, 2018

Kotun kasa da kasa da ke sauraron manyan laifuka ta ICC, ta wanke tsohon mataimakin shugaban kasar kwango Jean-Pierre Bemba, bayan da ya daukaka karan shari'ar farko da aka yi masa.

https://p.dw.com/p/2zBQP
Belgien Jean-Pierre Bemba Gombo in Brüssel
Hoto: Reuters/F. Lenoir

A shari'ar farko dai kotun mataki na farko ta ICC ya yanke masa hukunci dauri na tsawon shekaru 18 a gidan kaso kan zargin aikata manyan laifukan da mayakansa suka tafkan a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Sai dai kuma sashen daukaka kara na kotun ta ICC ya soke shari'ar farko sannan kuma ya wanke shi daga zargin da ake yi masa, a cewar alkalin kotun daukaka karan Christine van den Wyngaert, babban kuskuren da kotun ta farko ta tafka, shi ne ya shafe dukkan laifukan da ake zargin Bemba da aikatawa.

Tsohon hamshakin dan kasuwan na kasar Kwango da ya rikide ya koma madugun 'yan tawaye, an tuhume shi ne kan irin ta'asar da mayakansa na kungiyar MLC suka tafka a tsakanin shekara ta 2002 zuwa 2003, inda a shekara ta 2006 aka kama shi da laifin kashe-kashen jama'a da cin zarafin mata da mayakansa suka yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.