Kotun ICC ta gabatar da zargi akan shugaban yan tawayen COngo | Labarai | DW | 29.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ICC ta gabatar da zargi akan shugaban yan tawayen COngo

Masu gabatar da kara na kotun kasa da kasa dake birnin Hague, sun gabatar da takardun zargi kann aikata miyagun laifuka na yaki, akan tsohon shugaban yan tawaye na Congo, wato Mr Thomas Lubanga.

Kotun, a cewar rahotanni na zargin Mr Lubanga ne da tursasa yara yan shekara 10 daukar makamai domin yaki, a yankin Ituri a shekara ta 2002.

Mr Lubanga, wanda ke hannun jami´an kotun na kasa da kasa, a tun watan maris na wannan shekara, tuni ya karyata wannan zargi da ake masa.

Bayanai dai sun nunar da cewa, matukar kotun ta tabbatar da wannan zargi, Mr Lubanga zai kasance mutum na farko daya bayyana a gaban kotun, don amsa laifuffuka dake da nasaba da aikata miyagun laifuffuka.

Har ilya yau kotun ta ICC tace a shirye take ta tuhumi shugabannin kungiyyar yan tawaye ta LRA na kasar Uganda, bisa laifuffukan yaki da ake zargin su da aikatawa.