1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Hague na shirin yanke hukunci akan Charles Taylor

April 25, 2012

Liberia ta bukaci zaman lafiya gabanin hukuncin kotun duniya dake Hague akan Charles Taylor

https://p.dw.com/p/14l1p
In this image made from television broadcast Tuesday, July 14, 2009 by the International Criminal Court, former Liberian President Charles Taylor, address the U.N. backed Special Court for Sierra Leone. Wearing a gray double-breasted suit and dark glasses, Taylor spoke confidently as he introduced himself to the three-judge panel as the 21st president of the Republic of Liberia. It was his first time on the witness stand. Taylor is charged with 11 counts of murder, torture, rape, sexual slavery, using child soldiers and spreading terror during Sierra Leone's 1991-2002 civil war. He is the first African leader to stand trial for war crimes. (AP Photo/ICC)
Hoto: AP

Gwamnatin kasar Liberia ta bukaci jama'a su kwantar da hankula su kuma zauna lafiya gabanin hukuncin da kotun musamman ta kasa da kasa za ta yanke a ranar Alhamis akan shari'ar tsohon shugaban Liberia Charles Taylor. Shugabar kasar ta Liberia Ellen Johnson Sirleaf a cikin wata sanarwa ta bukaci jama'a su cigaba da yiwa kasar addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali. A ranar Alhamis din nan ne dai kotun ta Majalisar Dinkin Duniya dake Hague za ta baiyana hukunci akan shari'ar ta Charles Taylor wadda aka shafe shekaru shida ana gudanarwa. Ana dai tuhumar Charles Taylor ne da laifukan yaki goma sha daya wadanda aka aikata a lokacin yakin Saliyo a tsakanin shekarun 1991 zuwa shekara ta 2002.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu