Kotun dake tuhumar Saddan ta na da sabon alkali | Labarai | DW | 23.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun dake tuhumar Saddan ta na da sabon alkali

Schröder da Merkel a mahawara ta telebijin

Schröder da Merkel a mahawara ta telebijin

Kotun dake sauraron shari´ar tsohon shugaban kasar Iraqi, wato Saddam Hussain , ta dana sabon alkalin da zai shugaban ci zaman kotun.

Nadin Rauf Rashid Abdelrahman dai dan kabilar kurdawa, ya biyo bayan murabus din da alkalin kotun na farko ya yi ne, wato Rizkar Mohd Amin, bisa sukar da gwamnatin kasar tayi masa na cewa yana saka ci wajen gudanar da aikin sa.

A dai gobe talata ne ake sa ran ci gaba da sauraron shari´ar ta Saddam Hussain da mukarraban nasa guda bakwai.

Kotun dai ta Birnin Bagadaza, na zargin Saddam Hussain ne da mukarraban nasa da laifin yin kisan gilla ga daruruwan mutanen a yankin Dujail a shekara ta 1980.

Matukar dai aka same su da wannan laifi to babu makawa hukuncin kisa ya hau kann su.

A waje daya kuma bayanai sun nunar da cewa wadanda suka yi garkuwa da yar jaridar nan data fito daga Amurka, wato Jim Carroll an sako ta.

Jim Carrol ta kasance a hannun wadanda sukayi garkuwa da itan ne a tun ranar bakwai ga watan nan da muke ciki.