Kotun Amirka ta sake watsi da dokar baki | Labarai | DW | 16.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Amirka ta sake watsi da dokar baki

Alkalin Kotun birnin Hawaii ya ce illolin hana baki shiga Amirka sun fi alfanunsa yawa don haka kamata ya yi a hana dokar aiki.

Wata kotu a Amirka ta yi watsi da sabuwar dokar da shugaba Donald Trump ya rattaba wa hannu, don hana 'yan kasashen Musulmai  shiga Amirkar. Wata kungiyar lauyoyin jihohin Amirka ce dai ta shigar da wannan kara kuma ta cimma nasara.Alkalin kotun da ke a birnin Hawaii, Darren Watson ya yanke hukuncin ne bisa dogaron cewar dokar ba za ta haifar wa kasar komai ba, illa kyama ga Musulmai. A cewar lauyoyin hana Musulmi shiga Amirka ka iya haifar da wariya sannan kuma fannin yawon bude ido na kasar zai iya samun koma-baya da kuma samun karancin ma'aikata a kasar.

To sai dai shugaba Trump ya bayyana al'amarin da wani abin da ba a taba yin irinsa ba a shari'ance,  inda ya lashi takobin kalubalantar shari'ar a kotun koli. Wannan dokar dai ta shafi kasashen Iran ne da Libya da Syria da Somalia da Sudan da kuma kasar Yemen.