Kotu ta yanke hukunci a kan Faisal Shazad | Labarai | DW | 05.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta yanke hukunci a kan Faisal Shazad

An yanke masa hukuncin daurin rai da rai bayan da ya yi yunkurin kai hari a dandalin Time Square da ke birnin New - York.

default

An yanke hukuncin ɗaurin rai da rai a kan Faisal Shahzad, haifaffen Pakistan ɗin nan mai takardar zama ɗan ƙasar Amurka, wanda ya yi yunƙurin kai harin bam ɗin da baiyi nasara ba a dandalin Times Square da ke birinin New -York na ƙasar Amuirka.

Alƙalin kotun Miriam Goldman Cedarbaum ta yanke wannan hukuncin ne bisa tuhumarsa da aka yi da laifuka goma, waɗanda suka haɗa da ta'addanci da yin amfani da makamai ba bisa ƙa´ida ba.

Shahzad mai shekaru 30 da haihuwa ya ɗauki alhakin ƙaddamar da shirin, wanda da ya yi nasara, to kuwa da zai yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 40. Shahzad ya yi wannan yunƙurin ne a ranar ɗaya ga watan Mayun da ya gabata.

Jami'an tsaro sun kama Shahzad ne kwanaki ukku bayan da ya kai harin, yayin da ya ke ƙoƙarin barin Amurka a sace, cikin wani jirgin saman da zai nufi birnin Dubai a haɗɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Ya bai wa jami'an tsaron haɗin kai tun sa'adda su ka kama shi, kuma ya amince da laifukan da aka tuhume shi da su, waɗanda ya ce ya yi ne domin nuna adawarsa da yadda ƙasar Amirka ta mamaye ƙasashen Afganistan da Irak.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Ahmed Tijjani Lawal