1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta wanke shugaban Brazil daga zargi

Mouhamadou Awal Balarabe
June 10, 2017

Shugaban kasa Michel Temer zai ci gaba da jan ragamar mulkin Brazil bayan da kotun kararrakin zabe ta yi watsi da zargin cin hanci da magudin zaben 2014 da aka yi masa.

https://p.dw.com/p/2eRTz
Brasilien Präsident Michel Temer in Brasilia
Hoto: picture-alliance/dpa/PR/M. Correa

Kotun da ke sauraren kararrakin zabe a Brazil ta wanke shugaban kasa Michel Temer daga zargin da aka yi masa na cin hanci da magudi a yakin neman zaben 2014, lamarin da ya sashi tsallake matakin tsigewa daga mukamin sa. Bayan da suka shafe kwanaki hudu na muhawa kan wannan batu, hudu daga cikin alkalai bakwai na kotun sun amince Temer ya ci gaba da mulki bayan da suka yi watsi da zargin da ake masa.

Dama dai Michel Temer ya sha alwashin ci gaba da jan ragamar mulkin Brazil har zuya karshen wa'adinsa a 2018, duk da bakin jinin da yake fama da shi. Sai dai kuma shugaban na Brazil bai rabu da Bukar ba, saboda kotun kolin kasar na gudanar da wani bincike na daban a kan shi. Sannan 'yan majalisa da dama sun shigar da daftarin yankar kauna na neman kada kuri'ar neman tsige shi. Tuni ma jam'iyyar PSDB da ke kawance da gwamnati ta bayyana aniyar raba gari da Temer yayin wani taron kolin da za ta gudanar a ranar Litinin mai zuwa.