Kotu ta soke zaben Gwamnan Jihar Adamawa a Najeriya | Labarai | DW | 15.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta soke zaben Gwamnan Jihar Adamawa a Najeriya

Kotun dake sauraren ƙararrakin zabe a jihar Adamawa a Najeriya ta soke zaɓen Gwamnan jihar, wato Admiral Murtala Nyako.Kotun ƙarkashin alƙali Akinwole ta ce ta soke zaɓen ne, a sabili da karan tsaye da ya yi ne ga dokokin zaɓe a ƙasar.Kotun ta kuma bukaci hukumar zaɓe ta ƙasa, wato INEC da ta gudanar da wani sabon zaɓen nan da kwanaki 90 masu zuwa. A yanzu haka dai Mr Nyako nada kwanaki 21, na ko dai ya ɗaukaka ƙara ko kuma ya sauka daga muƙaminsa.Jim kaɗan da yanke hukuncin kafafen yaɗa labarai sun rawaito ɗan takarar Jam´iyyar Ac na Gwamna a jihar, Alh Ibrahim Bapetal na cewa har yanzu da sauran rina a kaba.