Kotu ta dakatar da sakin aure a Falasdinu
May 28, 2017Talla
Cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban alkallan na Falasdinu ya ce ya dauki wannan mataki ne ta sabili da abubuwan da suka gani a shekarar da ta gabata, inda mutane suka yi ta sakin matayensu sannan daga bisani suka yi nadama.
A cikin wannan wata dai na Azumin Ramadan, wasu mutanen da ba su da abinci, ko kuma ba su samu sigarin da suka zuka ba, kan tayar da rikici a gidajensu, inda wani lokacin sukan daukan mataki na gaggawa na saki.