1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta dage yanke hukunci ga Ahmed Abba

Mouhamadou Awal Balarabe
April 20, 2017

Kotu soja ta kasar kamaru ta tsayar da 24 ga Afirilu a matsayin ranar da zata sanar da hukuncin da ta yanke wa wakilin sashen Hausa na RFI Ahmed Abba bisa zargin hada kai da 'yan ta'adda a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/2be9l
Karte Kamerun Extrême-Nord Englisch

Kotun soja ta kasar kamaru ta dage hukuncin da ya kamata ta yanke wa wakilin sashen Hausa na RFI Ahmed Abba dangane da tuhumar da take masa ta hada kai da 'yan ta'adda wajen cutar da kasa. Sai dai lauyansa wanda ake tuhuma Barrister Charles Tchoungang ya nuna mamaki dangane da matakin saboda yau (20.04.2017) ne ranar karshe da doka ta kayyade ta yanke wannan hukunci. Kotun dai ta tsayar da 24 ga watan Afirilu wajen sanar da hukucin da ta yanke wa dan jaridan da ya shafe shekaru 21 a gidan yari.

A ranar 25 ga watan Julin 2015 aka cafke Ahmed Abba a Maroua da ke arewacin kamaru bisa zargin rashin tona asirin 'yan ta'adda da kuma yaba ayyukansu na ta'addanci a cikin rahotannin da ya hada. Sai dai dan jaridar ya yi watsi da duk zarge-zargen da ake masa.  Fiye da mutane goma ne aka yanke wa hukuncin kisa a kamaru tun bayan da doka kan ta'addanci ta fara aiki a kasar shekaru biyun da suka gabata.