1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Switzerlan ta tasa keyar dan kasar Rwanda dake zaman mafaka

October 27, 2006
https://p.dw.com/p/BueF

Babbar kotun kasar Switzerland ta tabbatar da bada umurnin maida dan kasar Rwanda Fulgence Niyonteze da ake zargi da manyan laifukan yaki a lokacin kisan kiyashi na Rwanda a 1994.

Kotun soji ta Switzerlan ta kama Niyonteze dan shekaru 42 da haihuwa,kuma tsohon magajin garin Mushubati wadda ke da tazarar kilomita 5o daga birnin Kigali, da laifukan kisan kai,da yunkurin kisan kai da kuma ingiza yin hakan da wasu laifukan yakin na daban a rikicin kasar Rwanda da yayi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 500,000 yawancinsu yan kabilar Tutsi da Hutu masu sassucun raayi.

Tunda farko Niyonteze ya nemi mafakar siyasa a kasar Switzerland,inda kuma kotun kasar ta yanke masa hukuncin dauri shekaru 14 bisa laifukan daya aikata,amma yanzu haka ta yanke hukuncin cewa kasar ba zata bada mafaka ga wanda ya aikata laifukan yaki ba.