Kotu a Saliyo ta kama shugabannin yan tawaye biyu da laifukan yaki | Labarai | DW | 02.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Saliyo ta kama shugabannin yan tawaye biyu da laifukan yaki

Kotun musamman mai sauraron kararrarkin yaki mai dauke da goyon bayan MDD a Saliyo ta kama wasu tsoffin shugabannin tawaye biyu na saliyo da laifukan yaki,sai dai ta kuma wanke su daga wasu manyan laifuka na take hakkin dan adam.

Moinina Fofana da Allieu Kondewa shugabbanin yan tawaye ne na kungiyar Civil Defence Forces,mai goyon bayan shugaba Ahmed Tejjan kabbah wacce ta yaki yan tawaye a yakin basasar kasar a 1991-2002.

Kabbah dai sai sauka daga mulki bayan zaben ranar 11 ga watan Agusta inda mataimakinsa ake sa ran zai gaje shi.