Kotu a Nigeria tace Alh Atiku Abubabar zai tsaya takara | Labarai | DW | 17.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Nigeria tace Alh Atiku Abubabar zai tsaya takara

Hukumar zabe a Nijeriya, ta baiwa mataimakin shugaba Atiku Abubakar damar tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za’a gudanar ranar asabar, amma ana tababa akan ko sunana Atiku Abubakar zai samu shiga cikin jerin sunayen masu takarar kujerar shugaban kasa kafin zaben, sabada karancin lokaci. An tsayar da maganar sake saka shi cikin masu takara bayan kotun koli a jiya, ya yanke hukumci da cewar hukumar zabe bata da ‚yancin dakatar da shi daga takara akan zargin cin hanci da rashawa. Alhaji Abubakar Atiku na daya daga wadanda suka kafa jam’iyar PDP ta shugaba Olusegun Obasanjo, kafin sabannin ra’ayi da ya hardasa musu rikice rikice.