1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Jordan ta yanke hukuncin kisa akan Al-Zarqawi

Wata kotun soji a kasar Jordan,ta yanke hukuncin kisa akan wasu mutane 9,ciki kuwa har da Abu Musab al-Zarqawi,bisa laifin shirya kai harin makamai masu guba akan kasar ta Jordan.

An yanke wannan hukunci na yau ne ba tare da Al-zarqawi da wasu 3 da ake tuhuma tare da shi suna kotu ba.

Amma babban wanda ake zargi,Azmi al-Jayousi da sauran wadanda ake zargi 4 suna a kotun lokacinda alkali ya yanke musu hukuncin kisa bisa yunkurin kai hari a Jordan a 2004.

An dai zargi wasu mutane 13 da laifin shirya manakisar fesa sinadare masu guba da ka iya kashe dubban mutane a wurare da dama cikin Jordan.