Kotu a Jamus ta yanke hukunci kan wasu Larabawa uku | Labarai | DW | 06.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Jamus ta yanke hukunci kan wasu Larabawa uku

Wata kotu a nan Jamus ta yanke hukuncin kan wasu larabawa uku bisa laifin shirya manaƙisar tura ƙudi ga ƙungiyar Al Ƙaida. An kama yan Syria biyu da wani Bapalasɗine da laifin zama membobin ƙungiyar Osama bin Laden ta Alƙaida. An yakewa larabawan hukuncin ɗaurin tsakanin shekaru uku zuwa 9 a gidan yari. Ƙarkashin dokar wadda aka kafa bayan harin 11 ga watan Satumba a Amurka,kotun ta kuma kama mutanen da laifin ƙoƙarin mallakar kayayyakin ƙera makaman nukiliya tare da ɗaukar sabbin membobi ga ƙungiyar don kaiwa harin kunar bakin wake a Iraki