Kotu a Ivory Coast zata mika Fofana izuwa kasar Faransa | Labarai | DW | 28.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Ivory Coast zata mika Fofana izuwa kasar Faransa

Hedkwatar Kungiyar Hadin Kan Turai a birnin Brussels.

Hedkwatar Kungiyar Hadin Kan Turai a birnin Brussels.

Wata kotu a kasar Ivory Coast ta fara shirye shiryen mika mutumin nan da ake zargi shine ya kashe wani bani yahudu, mai suna Ilan Halimi, izuwa kasar Faransa.

Jami´an yan sanda a birnin Abijan sun tabbatar da cewa tuni Youssef Fofana wanda dan asalin kasar Faransa ne ya amsa laifin cewa shine ya aikata wannan zargi da ake masa akan Ilan Halimi dan shekara 23 bayan yayi garkuwa dashi.

Rahotanni dai sun nunar da cewa bayan cafke Fofana da yan sanda suka yi a ranar larabar data gabata, da yawa daga cikin Faransawa sun gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da wannan aiki daya aikata, da cewa na daga cikin munanan aiyuka na take hakkin bil adama.