1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Hague ta yanke hukunci kan wanda ya sayrwa Saddam Sinadarai

December 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvFM

A yau wata kotu a Hague,ta yanke hukuncin daurin shekara15 a gidan yari akan,wani dan kasuwan kasar Frans van Anraat,bisa laifin taimakon aikata laifukan yaki,ta hanyar sayarda sinadarin da aka yi anfani da shi wajen kera makamai masu guba da tsohuwar gwamnatin Saddam Hussein tayi anfani da su wajen kaiwa hari kan kauyukan Qurdawa.

Tun da farko kotun tace,duk da cewa an tabbatar cewa Saddam ya aikata kisan kiyashi a shekarun 1980,kotun ta wanke van Anraat daga laifin kisan kai tunda a cewarta ba shi da masaniyar cewa Saddam din zai yi anfani da sinadarin wajen kashe jamaarsa.

Wannan shine karo na farko da kotun ta yanke hukuncin cewa shugaban na Iraqi ya aikata laifin kisan kiyashi a Iraqi,a 1988 inda aka kashe Qurdawa fiye da 5,000 a garin Halabja.