Kotu a China ta zartar da hukunci kan wani fitaccen lauya | Labarai | DW | 22.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a China ta zartar da hukunci kan wani fitaccen lauya

Wata kotun kasar China ta zartas da hukuncin dauri na shekaru 3,kan wani shahararen lauya dan kasar mai paputukar kare hakin yan adam Gao Zhisheng.

Mahukuntan kasar ta China dai suna zargi Mr.Gao ne da laifin bata sunan kasar,wanda suka bayyana yayi ne wajen wallafa batutuwa kan siyasa ta yanar gizo ta internet da kasashen ketare.

Kotun har ila yau ta hana mr.Gao damar nua kin amincewa a kann wannan hukunci.

Mr.Gao Zhisheng yana tsare ne tun watan Agusta lokacin da gwamnatin ta tashi kann lauyoyi kamarsa.