Kotin Kolin Jamus ta yi belin Munnir El Mottassadek | Labarai | DW | 07.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotin Kolin Jamus ta yi belin Munnir El Mottassadek

A wani mataki na ba zata, a dazun nan ne, kotu a birnin Hamburg ta yi belin Munir El Mottassedek,dan assulin kasar Marroko, mutum daya tilo, da kotu ta yanke wa hukuncin daurin shekaru 7, bayan an tuhume shi, da hannu a cikin harin ta´adancin ranar 11 ga watan satumba a kasar Amurika.

A watan Ogust ne da ya wuce, kotu a birnin Hamburg na nan Jamus, ta yanke masa wannan hukunci.

Babbar kolin kasar Jamus, ta yanke shawara sallamar Munnir El Mottassadek bayan ya daga kara.

Binciken da kotu ta gudanar ya wanke shi daga duk wata tuhuma.

Zai ci gaba da zama cikin yanci har lokacin da hukuncin karshe zai bayyana daga kotun Tarayya.