1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Kudu ta yi gwajin makamai

Ramatu Garba Baba
September 4, 2017

Koriya ta Kudu ta kaddamar da wani atisayen gwajin makamai a kusa da tekun da ke kan iyakar kasar da Koriya ta Arewa a wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/2jIaF
Nordkorea - Raketentest
Hoto: Reuters/KCNA

 Atisayen gwajin makaman a cewar ma'aikatar tsaron kasar gargadi ne ga makwabciyar ta Koriya ta Arewa bisa gwajin makamin nukiliyar da ta yi a ranar Lahadi wanda shi ne karo na shida da kasar ke yin gwajin.

Ana zargin Koriya ta Arewa da yin gwajin wani makamin kare dangi da kwararru suka alakanta alamun motsin kasa mai karfin gaske da aka ji a sakamakon gwajin, kafin wannan gwajin Koriya ta Arewa ta soma  fitar da wata sanarwar inda a ciki ta ke cewa ta hada wani babban bam wanda za a hada da makami mai linzami da za a iya harbawa daga nahiya zuwa nahiya, batun shirin nukiliyar Koriya ta Arewa da kuma gwaje-gajen da ta ke yi na makamai masu linzami da ke cin dogon zango na ci gaba da haifar da fargaba a tsakanin manyan kasashen duniya, Amurka ta soki gwajin da Pyongyang ta yi da cewa shiri ne na tayar da zaune tsaye.