Koriya ta arewa tace takunkumi da aka dora mata yaki aka kaddamar akanta | Labarai | DW | 17.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta arewa tace takunkumi da aka dora mata yaki aka kaddamar akanta

Koriya ta arewan ta baiyana takunkumi da komitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya dora mata da cewa yaki ne aka kaddamar akanta,ta kuma yi gargadin cewa,tana sa ido taga musamman mataki da Amurka zata dauka.

Jakadan Amurka Christopher Hill ya kai ziyara Koriya ta kudu domin shawo kanta ta kara matsa kaimin takunkumi da aka dorawa koriya ta arewa.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka kuma,Condoleeza Rice wadda nan gaba cikin wannan mako zata ziyarci Koriya ta kudu Japan da Sin,tayi gargadi ga kasar Iran cewa ya kamata ta dauki takunkumin da aka dorawa Koriya ta arewa a matsayin wani abinda zatayi tunani akai.