1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta yi nasarar gwajin makami

Gazali Abdou TasawaApril 24, 2016

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya bayyana gamsuwarsa da abin da ya kira nasarar da kasar ta yi wajen gwajin harba makami mai linzami daga teku zuwa doran kasa a ranar Asabar.

https://p.dw.com/p/1IbaP
Südkorea Berichterstattung über erneuten nordkoreanischen Raketentest
Hoto: Imago/Xinhua

Kafofin yada labarai na kasar ta Koriya ta Arewa dai sun ruwaito cewa shugaba Kim Jong-Un ya ce daga yanzu a ko yaushe kasarsa na iya harar biranen Seoul na Koriya ta Kudu da na Washington a Amirka a duk lokacin da ta yi niyar yin hakan.

Sai dai ministan tsaron Koriya ta Kudu ya bayyana cewa gwajin makamin da Koriya ta Arewar ta yi a wannan Asabar bai yi nasara ba, domin kuwa makamin ya fadi ne a cikin ruwan tekun Japan wanda ke nufin cewa bai wuce tafiyar nisan kilomita 30 ba da ya fadi.

Amirka da Birtaniya dai sun yi tir da Allah wadai da gwajin makamin wanda suka ce ya keta haddin kudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya haramta gwajin makami mai linzami.